16 Afirilu 2026 - 22:55
Source: ABNA24
Asiri Yana Ƙara Bayyana Kan Iran Ɓarnar Yaƙi Akan Iran Ya Haifar Ga Amurka

Hotunan tauraron dan adam sun nuna lalacewa da barnar kayan aikin sojin Amurka na biliyoyin daloli.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa:The Daily Mail ta fitar da bincike da ke nuna cewa Ma'aikatar yakin Trump ba ta faɗi gaskiya game da girman barnar da rikicin da aka yi da Iran ya yi ba. Domin hotunan taurarin ɗan adam da aka samu sun nuna girman barna da mummunar lalacewa ga kayan aiki masu mahimmanci, ciki har da manyan jiragen yaƙi masu ci gaba da jirage marasa matuki masu tsada da kayan aiki a sansanonin yanki.

Hotunan tauraron dan adam na sansanonin jiragen sama a Jordan, Kuwait da UAE sun nuna lalacewar jiragen F-35 guda uku da lalacewar jiragen jefa bama-bamai nau'in B-21 da jiragen ruwa da ƙananan jiragen marasa matuka na ruwa. Hotunan tauraron dan adam daga tashar jiragen ruwa na Fujairah da kudanci sun nuna kona manyan jiragen tankunan mai da aka yi niyya ayi aiki da su don tallafawa ayyuka na dogon lokaci. An kiyasta darajar man da aka yi asarar shi kadai ya haura dala miliyan 800.

Your Comment

You are replying to: .
captcha